Najeriya: Adadin Ma’aikatan Kiwon Lafiya Da Suke Kamuwa Da Corona Yana Karuwa

A cikin wani bayani da hukumar
dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya ta
fitar, ta bayyana cewa akalla ma’aikatan kiwon lafiya 75 suka kamu da cutar
Korona a makon jiya a fadin Najeriya.
A lokacin da yake zantawa da manema
labarai jiya a birnin Abuja fadar mulkin tarayyar Najeriya, shugaban hukumar NCDC
ya bayyana cewa, ana samun kamruwar adadin ma’aikatan kiwon lafiya da suke
kamuwa da cutar corona a Najeriya, wanda kuma hakan abin damu ne matuka.
Ya ce gwamnati tana kokari domin
ganin cewa ma’aikatan kiwon lafiya sun samu kariyar da ta dace, musamman
wadanda suke kula da masu dauke da cutar corona, amma babbar matsalar ita ce
babu wadatattun kayan aiki na kariya.
Shugaban hukumar ta NCDC ya ce daga
yanzu suna da shirin fara yin amfani da tsarin gwaji na nan take wato ‘Rapid
Diagnostic Test Kits wajen yi wa mutane gwajin cutar a asibitoci, wanda ya ce
hakan zai taimaka matuka wajen kare ma’aikatan kiwon lafiya.
Ya ce da farko za a fara yin amfani
da na’urar yin wannan gwaji ne a Abuja, inda za a fara horas da malaman kiwon
lafiya kan yin aiki da ita, daga bisani kuma za a rarraba ta zuwa sauran
cibiyoyin kiwon lafiya na kasa.
015