Iran Ta Bukaci Faransa Ta Daina Nuna Bangaranci A Game Da Yarjejeniyar Nukiliya

2021-01-31 10:12:14
Iran Ta Bukaci Faransa Ta Daina Nuna Bangaranci A Game Da Yarjejeniyar Nukiliya

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bukaci kasar faransa da ta daina nuna bangaranci game da yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a 2015.

Wannan dai na a matsayin maida martanin Iran ne game da kalamman da shugaban kasar Faransar Emanuel Macron ya firta a wata hira da tashar Al Arabiya, na cewa duk wata sabuwar tattaunawa da za’ayi da Iran, tana bukatar a sanya dukkan kasashen yankin har da Saudiyya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Saeed Khatibzadeh, ya yi fatali da duk wani yunkuri na sake tattaunawa ko kuma canza fasalin yarjejeniyar ta 2015, tare da kira ga shugaba Macron da ya daina daukan bangaranci ko kuma firta kalamai marar digi game da yarjejeniyar.

Iran, ta kuma sake nanata cewa game da batun sabawa yarjejeniyar, Amurka ce ta fara, don haka ita ce ya kamata ta fara dawowa domin nuna da gaske ta ke game da yarjejeniyar.

A shekarar 2015 ne Iran, ta cimma yarjejeniyar ta nukiliya tsakaninta da kasashen Amurka, Biritaniya, Faransa, Rasha, China da kuam Jamus, saidai daga bisani a shekarar 2018 Amurka karkashin tsahuwar gwamnatin Donald Trump ta fice daga yarjejeniyar tare da kakabawa Iran da sabbin takunkumai, lamarin da ya sanya ita ma Iran daga bisani ta jingine aiki da wasu bangarori da yarjejeniyar ta kunsa ciki har da batun tace sinadarin uranium.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!