CHAN 2020 : Kamaru Da Mali Sun Tsallake Wasan Daf Da Na Karshe

2021-01-31 09:28:54
CHAN 2020 : Kamaru Da Mali Sun Tsallake Wasan Daf Da Na Karshe

A ci gaba da gasar cin koshin Afrika na ‘yan wasan kwallon kafa dake taka tamaula a cikin gida dake gudana a Jamhuriyar Kamaru, kasashen Mali da Kamaru sun yi nasara tsallakewa a wasan daf da na karshe.

A zagayen kwata final da suka buga a jiya Asabar, Kamaru mai masaukin baki ta lallasa DRC, da ci (2-1).

A nan gaba kamaru zata kara da ko dai Morocco ko Zambia a wasan daf da na karshe.

Ita mai dai Mali ta yi nasarar tsallakewa a wasan gab da na karshe, bayan da doke Congo, a budun daga kai sai mai tsaron gida, (5-4) bayan da suka tashi ba tare da an zura kwallo ba (0-0), a mintina 90 da aka kayyade, har zuwa karin lokaci na mintina 15 sau biyu.

Nan gaba Mali zata fafata da Guinea ko Rwanda a wasan daf na karshe.

Yau Lahadi ne ake fafatawa a zagayen kwata final tsakanin Morocco da Zambia, sai kuma Guinea da Rwanda.


024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!