Najeriya:Buhari Ya bukaci Majalisar Dokokin Kasar Ta Amince Da Sabbin Shuwagabannin Rundunonin Sojojin Kasar Da Ya Nada

2021-01-29 20:42:52
Najeriya:Buhari Ya bukaci Majalisar Dokokin Kasar Ta Amince Da Sabbin Shuwagabannin Rundunonin Sojojin Kasar Da Ya Nada

Shugaba muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya rubutawa majalisar dokokin kasar wasika, inda yake bukatar ta amince da sabbin shuwagabannin rundunonin sojojin kasar da ya nada.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Femi Adesin kakakin fadar shugaban kasa yana fadar haka a wani rahoton da ya sanyawa hannu.

Labarin ya kara da cewa shugaban ya aikewa shugaban majalisar dattawan kasar Ahmad Lawal wasikar ne a ranar 27 ga wannan watannan da muke ciki.

Yan Najeriya da dama, sun dade suna kokawa kan tabarbarewar harkokin tsaro a kasar, tare da bukatar shugaban ya canza hafsoshin sojojin kasar kasar, wanda bai tannata ba sai a cikin makon da ya gabata.

Sabbin Shuwagabannin rundunonin wadanda aka nada dai sun hada da Manjo Janar Lucky Irabor, Manji janar Ibrahim Attahiru, Rear Admiral Auwal Gambo, da kuma Isyaka Amao.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!