WHO : Sabon Nau’in Koronar Burtaniya Ya Yadu A Kasashe 70

2021-01-28 21:26:00
WHO : Sabon Nau’in Koronar Burtaniya Ya Yadu A Kasashe 70

Hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta ce sabon nau’in cutar korona na Biritaniya, ya samu yaduwa zuwa kasashe da yankuna 70 na duniya.

Wannan a cewar WHO, an samu bullar nau’in a cikin kasashe goma daga ranar 12 ga watan Janairun nan.

A sanarwar data fitar ranar Laraba, hukumar ta kuma ce waccen nau’in cutar ta covid-19 da aka gano a AFrika ta kudu, shi kuwa ya yadu a cikin kasashe da yankuna 31.

Shi kuwa nau’in cutar na Brazil ya yadu a cikin kasashe guda takwas.

Kawo yanzu dai masana na ci gaba da gudanar da bincike kan wadannan nau’ukan cutar ta Covid-19 da aka bayyana suna da hadarin yaduwa.

A ranar 22 ga watan Janairu, firaministan Biritaniya, Boris Johnson, ya bayyana nau’in da mai saurin yaduwa da kashi 30 zuwa 40 cikin dari idan aka kwatanta yaduwarsa da wancen nau’in cutar na farko da aka sani, koda yake hukumar ta WHO, ta ce tana nazarin bayanin.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!