Gwamnatin Biden Ta Dakatar Da Sayar Da Makamai Ga Saudiyya Da Kuma UAE

Sabuwar gwamnatin Amurka ta sanar da dakatar da sayar da makamai ga ƙasashen Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umurni tana mai cewa za ta yi dubi cikin lamarin tukun.
Sabon
sakataren harkokin wajen Amurkan Antony Blinken ne ya sanar da hakan a
ganawarsa da manema labarai ta farko tun
bayan da aka tabbatar da shi a bisa
wannan matsayin inda yace dubi cikin
hakan don a tabbatar da abin da aka cimma ɗin zai taimakawa siyasar Amurka da
kuma ciyar da siyasarta ta waje gaba ne.
Kafin
hakan ma dai jaridar The Wall Street
Journal ta ba da rahoton cewa gwamnatin
Joe Biden ɗin ta ba da umurnin dakatar da kwangilar sayar da makamai ga
ƙasashen biyu ta biliyoyin daloli da gwamnatin
Trump ɗin ta ƙulla ciki kuwa har da sayar da jirgin nan na F-35 na yaƙi
ga UAE ɗin.
Wannan mataki kuwa ya zo ne mako guda bayan rantsar da Biden ɗin a matsayin sabon shugaban Amurka wanda da man yayi alƙawarin sake dubi cikin alaƙar Amurka da Saudiyya. Tun bayan hawarsa karagar mulki dai ya soke wasu daga cikin umurni da kuma matakan da tsohuwar gwamnatin Trump ɗin ta ɗauka.