Yemen: Kawancen Amurka-Saudiyya Na Aikata Ta’addanci Na Haƙiƙa

Al’ummar
ƙasar Yemen sun bayyana cewar ta’addanci na haƙiƙa shi ne abin da haɗakar
Amurka-Saudiyya suke aikatawa a kan al’ummar ƙasar Yemen na killace su da hana
su dukkanin abubuwan da suke buƙata wajen gudanar da rayuwarsu.
Wannan
kalami yana cikin sanarwar bayan taron gangamin da aka gudanar ne a yau ɗin nan
a birnin Sana’ na ƙasar Yemen ɗin don amsa kiran da wasu ƙungiyoyi suka yi na
gudanar da wannan gangami a masayin ‘Ranar Duniya Don Goyon Bayan Al’ummar
Yemen’ inda yayin da suke mayar da martani ga matakin da Amurka ta ɗauka na
sanya ƙungiyar Ansarullah ta Yemen ɗin cikin ƙungiyoyin ta’addanci suka bayyana
cewar: ta’addanci na haƙiƙa shi ne abin da haɗakar Amurka-Saudiyya suke
aikatawa a kan al’ummar ƙasar Yemen.
Masu
gangamin sun ci gaba da cewa: Amurka ita ce take da alhakin dukkanin hare-haren
da Saudiyya da ƙawayenta suke kai wa ƙasar ta Yemen da kuma ci gaba da killace
al’ummarta don kuwa ita ce take ba su goyon baya da kum dukkanin wani taimako
da suke buƙata.
Masu
gangamin sun ce sanya ƙungiyar Ansarullah a cikin ƙungiyoyin ta’addanci na
duniya da Amurka ta yi wani lamari ne da ke nuni da gazawa da kuma shan kashin
Amurkan a gaban al’ummar Yemen.
A kwanakin baya ne dai ƙungiyoyi da cibiyoyi daban-daban suka yi kiran da a gudanar da gangami a yau ranar 25 ga watan Janairu a matsayin ‘Ranar Duniya Don Goyon Bayan Al’ummar Yemen’ don nuna goyon baya ga al’ummar Yemen ɗin da kuma yin Allah wadai da halin da aka sanya su ciki na yunwa da rashi da tsanani sakamakon yaƙin wuce gona da iri da Saudiyya da ƙawayenta bisa goyon bayan Amurka suka ƙaddamar kan ƙasar sama da shekaru biyar ɗin da suka gabata.
015