​Nujba: Zamu Mayar Yaki Da Ta’addanci A Cikin Kasashen Da Ke Daukar Nauyin ‘Yan Ta’adda

2021-01-23 18:48:32
​Nujba: Zamu Mayar Yaki Da Ta’addanci A Cikin Kasashen Da Ke Daukar Nauyin ‘Yan Ta’adda

Kungiyar gwagwarmaya ta Nujba a kasar Iraki ta bayyana cewa, za su mayar da yaki da ta’addanci a cikin kasashen da suke daukar nauyin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Kakakin kungiyar Nujba Nasr Al-shummari ya bayyana cewa, suna da cikakken bayani na sirri kan cewa, ‘yan ta’addan takfiriyya suna da shirin kutsawa a cikin wuraren ziyara na addini a birananin Karbala da Najaf da ke Iraki, domin aiwatar da ayyyukan ta’addanci kamar yadda suka yi a birnin Bagadaza a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya ce suna gargadin kasashen da suke daukar nauyin ‘yan ta’adda da suke kaddamar da wadannan hare-hare da su kwana da sanin cewa, idan suka ci gaba da turo ‘yan ta’adda a cikin kasar Iraki domin kashe al’ummar Iraki ta hanyar tayar da bama-bamai kamar yadda suka rika yi a ‘yan shekarun baya, to lamarin zai dawo cikin kasashensu.

Ya kara da cewa, suna masaniya kan cewa wadanda suka kai harin ta’addancin na kunar bakin wake, wanda ya kashe fararen hula fiye da talatin a birnin Bagadaza a ranar Alhamis da ta gabata, dukkaninsu ‘yan kasar Saudiyya ne.

Al-shummari ya ce, wadannan ‘yan ta’adda sun shigo cikin kasar Iraki ne ta barauniyar hanya a kan iyakokin Syria da Iraki, kuma dama suna daga cikin masu kai irin wadannan hare-haren ne a cikin kasar Syria.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!