Hukumomi A Faransa Sun Rufe Masallatai 9 A Fadin Kasar

2021-01-16 14:48:35
Hukumomi A Faransa Sun Rufe Masallatai 9 A Fadin Kasar

Hukumomi a Faransa, sun sanar da rufe masallatai guda tara a kasar, a wani mataki da hukumomin kasar suka ce na rashin bin ka’idodi ne.

Mafi yawan masallatan sun kasance a Paris babban birnin kasar.

Wata sanarwar da ma’aikatar cikin gidan kasar ta fitar ta ce an rufe masallatan sabodai da dalilan da suka hada da ka’idodin tsaro da kuma na gudanarwa.

Matakin dai na zuwa ne makwanni kadan bayan da kasar ta kaddamar da wani aikin sa ido a wuraren ibadar musulmin.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!