Trump Na Shirin Ficewa Daga Birnin Washington A Safiyar Laraba Kafin Rantsar Da Biden

Shugaban kasar Amurka mai barin gado
Donald Trump na shirin ficewa daga birnin Washington fadar mulkin kasar Amurka
da jijjifin safiyar ranar Laraba, kafin rantsar da zababben shugaban kasar Joe
Biden, inda zai nufi yankin Palm Beach da ke cikin jihar Florida.
Jaridar Washington Post ta bayar da
rahoton cewa, a daidai lokacin da ake cikin shirye-shiryen gudanar da babban
taron rantsar da zababben shugaban kasar Amurka Joe Biden a ranar Laraba mai
zuwa, Trump ya kammala shirinsa tsaf domin ficewa daga Washington da jijjifin
safiyar ranar ta Laraba, kafin rantsar da Biden.
Rahoton ya ce a daren Talata Trump
zai halarci wata dabdala da za a shirya masa ta bankwana a sansanin Anrews da
ke wajen birnin Washington, inda shi da mukarrabansa da kuma iyalansa za su halarci
wurin.
A cikin makon nan dai an ga motocin
daukar kaya suna ta jigilar kayayyakin Trump, inda ake fitar da su daga cikin
fadar White House zuwa wasu wurare na daban a cikin birnin Washington.
Trump dai ya sha alwashin cewa ba
zai halarci taron rantsar da sabon shugaban kasar Amurka ba, bisa zargin da ya
yi na cewa an yi masa magudi, inda a cikin makon da ya gabata ne ya tunzura
magoya bayansa suka kaddamar da farmakia
kan babban ginin majalisar dokokin kasar ta Amurka, tare da haifar da
tarzoma, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 da suka hada da jami’in
‘yan sanda guda.