Iran:Iran Da Sauran Kasashen Duniya Suna Fatan Amurka Ta Dauke Mata Takunkaman Tattalin Arzikin Da Aka Dora Mata

2021-01-15 15:11:50
Iran:Iran Da Sauran Kasashen Duniya Suna Fatan Amurka Ta Dauke Mata Takunkaman Tattalin Arzikin Da Aka Dora Mata

Jakadan kasar Iran a MDD Majid Takht Ravanchi ya bayyana cewa Iran da sauran kasashen duniya suna fatan sabuwar gwamnatin Amurka mai shigowa za ta dauke takunkuman da gwamnatin da za ta shude ta dora mata.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ta nakalto Takht-Ravanchi yana fadar haka a jiya ALhamis ya kuma kara da cewa, kafin haka dai an ji wasu kalamai masu nuna cewa gwamnatin Amurka mai kamawa zata koma cikin yarjejeniyar JCPOA ta kasar Iran..Amma jami’an gwamnatin kasar Iran da dama sun bayyana cewa komawar Amurka cikin yarjejeniyar JCPOA ba tare da daukewa kasar wadannan takunkuman ba, bai da wani amfani a wajenta.

Tun shekara ta 2018 ne gwamnatin shugaba Donal Trump ta fice daga yarjejeniyar ta JCPOA sannan ta dorawa kasar Iran abinda ta kira takunkuman

tattalin arzikin mafi muni a tarihin kasar. Da nufin tilastawa kasar shiga sabuwar tattaunawa dangane da shirye-shiryenta na makamashin nukliya da sauran

makamanta. Amma har wa’adin ikon gwamnatin ya cika ba ta cimma manufarta ba.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!