Siriya Ta Yi Tir Da Hare haren Isra’ila, Tare Da Kiran MDD, Ta Dauki Mataki

2021-01-14 21:32:52
Siriya Ta Yi Tir Da Hare haren Isra’ila, Tare Da Kiran MDD, Ta Dauki Mataki

Gwamnatin Siriya ta ce ta kosa da hare haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kai mata, tare da kira ga MDD, data dauki matakin mai tsauri domin kawo karshen sake aukuwar hakan.

A cewar kamfanin dilancin labaren SANA, Isra’ila ta kai jerin hare hare n sama a gabashin kasar a kusa da iyaka da Iraki, da sanyin safiyar ranar Laraba data gabata.

Hare haren a cewar labarin an kai su ne kan yankunan Dayr al-Zawr da kuma al-Bukamal.

A cikin wasikar data aikewa babban sakataren MDD, da kuma shugaban kwamitin tsaron MDD, ma’aikatar harkokin wajen Siriya ta ce tsokanar ta Isra’ila ta wuce gona da iri a baya bayan nan inda har ta kai ga kisan jama’a.

Siriya, ta bukaci kwamitin tsaron MDD, da ya dauki mataki kamar yadda dokokin MDD, suka tanadar, domin dora alhakin kashe kashen al’ummar Siriya dake faruwa ga Isra’ila.

Kikanin muatne 57 ne aka rawaito cewa sun rasa rayukansu a jerin hare haren Isra’ilar na baya baya nan a yankin Deir ez-zor da Al-Bukamal.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!