Iran: An Mikawa Rundunar Sojin Ruwa Katafaren Jirgin Ruwa Na Yaki A Yau

2021-01-13 14:40:17
Iran: An Mikawa Rundunar Sojin Ruwa Katafaren  Jirgin Ruwa Na Yaki A Yau

A safiyar yau Laraba ce aka yi bikin mikawa sojojin ruwa na Jumhuriyar Musulunci ta Iran wani kataparen jirgin ruwan yaki mai suna “Makran”, wanda kuma shi ne jirgin ruwan yaki mafi girma wanda kwararu na JMI suka gani a cikin gida.

Majiyar muryar JMI ta bayyana cewa manya –manyan jami’an sojojin kasar sun halarci wannan bikin akwai Janar Mohammad Bakiri babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran.

Makran yana da nauyin ton 121, sannan yana da tsawon mita 228, fadin mita 42 sannan zurfin mita 21.5.

Banda haka jirgin yana da wuraren saukar jiragen sama masu saukar ungulu har hudu, yana da kayakin aikin soje na zamani, da bindigigi masu sarrafa kansa, da kuma cilla makamai masu linzami daban-daban, har’ila yau zai iya samfani da kanan kwale-kwale da jiragen sama wadanda ake sarrafasu daga nesa.

Aikin jirgin ruwan yakin Makran shi ne yin sintiri da kuma raka jiragen ruwa a cikin tekn Indiya zuwa mashigar Babul Mandan na kasar Yemen, da kuma Tekun maliya.

019

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!