​Faleh Fayyad: Takunkumin Amurka Ba Zai Iya Sa Mu Ja Da Baya Ba

2021-01-11 19:05:54
​Faleh Fayyad: Takunkumin Amurka Ba Zai Iya Sa Mu Ja Da Baya Ba

Babban kwamandan rundunar sa kai ta al’ummar Iraki Hash Al-shaabi, Faleh Fayyad, ya bayyana cewa; takunkumin da Amurka ta sanar da kakaba masa, ba zai iya mayar da su baya ba daga abin da suka sanya a gaba.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a wata ganawa da ta gudana a yau a tsakanin babban kwamandan rundunar sa kai ta al’ummar Iraki Hash Al-shaabi, Faleh Fayyad, da kuma shugaban majalisar tsaron kasa a Iraki Kasim Al-araji, bangarorin biyu sun jaddada wajabcin kara hada karfi da karfe domin cimma manufofi na al’ummar kasarsu.

Fayyad ya jaddada cewa, duk wani takunkumi na Amurka, ba zai iya karya gwiwarsu wajen ci gaba da yaki da ‘yan ta’addan Daesh ba, ko Amurka ta so hakan ko ba ta so ba, kuma rundunar Hashd Shaabi na nan daram kan bakanta, na cewa dole ne dukkanin sojojin Amurka su fice daga Iraki, kamar yadda kudirin majalisar dokokin kasar ta Iraki ya bukaci hakan.

Ya kara da cewa kakaba takunkumi da Amurka ta yi a kan bangarorin rundunar sa kai ta al’ummar Iraki da suka fattataki ‘yan ta’addan Daesh daga kasar, yana a matsayin cin zarafi ne ga dukkanin al’ummar Iraki, kuma za su kalubalanci hakan da dukkanin karfinsu.

Takunkumin Amurka a kan Faleh Fayyad ya fuskanci kakausar martani daga shugaban kasar Iraki Barham Saleh, gami da Firayi minista Mustafa Alkazimi da kuma shugaban majalisar dokoki Muhammad Halbusi, da sauran manyan jami’an tsaro gami da ‘yan siyasa, da sauran bangarori na al’ummar Iraki.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!