An Yi Ganawa Tsakanin Sudan Da AU Kan Batun Tekun Nilu

2021-01-10 21:07:16
  An Yi Ganawa Tsakanin Sudan Da AU Kan Batun Tekun Nilu

Wasu jami’an kasar Sudan da tawagar kwararrun kungiyar tarayyar Afrika AU, sun gudanar da wani taron tattaunawa game da batun gina madatsar ruwan Habasha.

Wata sanarwa da ma’aikatar noman rani da albarkatun ruwa ta Sudan ta fitar ta ce, tawagar wakilan Sudan masu tattauna batun madatsar ruwan, sun gudanar da tattaunawar hadin gwiwar da yammacin ranar Asabar tare da tawagar kwararrun AU.

Tattaunawar na zuwa ne a matsayin martani game da kiran da Sudan tayi ga kwararrun kungiyar AU bisa muhimmiyar rawar da za su taka wajen shiga tattaunawar sulhun tsakanin kasashen Sudan, Masar da Habasha domin bayar da gudunmawa a zagaye na biyu na shirye-shiryen samar da yarjejeniyar fahimtar juna wanda kasashen uku suka amince da shi a taron da ya gudana na lokacin baya na bangarori shida.

A cewar sanarwar, taron ya tattauna muhimmancin tsara jadawali game da rawar da kwararrun AU za su taka, ta kara da cewa, Sudan ta jaddada bukatar cewa kamata ya yi AU ta taka muhimmiyar rawa a matsayinta na shugaba fiye da yadda ta saba takawa a zaman tattaunawar da aka gudanar a lokutan baya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!