Rikici Ya Barke A Majalisar Kasar Ghana A Yayin Zaman Zaban Kakakin Majalisar

2021-01-07 20:53:20
Rikici Ya Barke A Majalisar Kasar Ghana A Yayin Zaman Zaban Kakakin Majalisar

Sojoji a kasar Ghana sun yi amfani da karfi wajen kawo karshen wani rikici da ya barke a majalisar kasar tsakanin ‘yan jami’iyyun kasar a daidai lokacin da ake shirin zaban sabon kakakin majalisar.

Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne lokacin da wani dan majalisa dan jam’iyyar da ke mulki a kasar yayi kokarin yin awun gaba da akwatin zabe a yayin da ake shirin kada kuri’ar zaban kakakin majalisar, lamarin da ya dau sa’oi ana ta rikici har sai da sojoji suka shigo suka kwantar da rikicin.

‘Yan majalisa magoya bayan jam’iyyar adawa sun zargi ‘yan majalisa daga jam’iyya mai mulki da haifar da fitina da kin bin doka da oda.

Sabuwar majalisar dai ta rabu kusan gida biyu tsakanin manyan jam’iyyu biyu na kasar wato jam’iyya mai mulki ta shugaba Nana Akufo Addo da kuma jam’iyyar National Democratic Congress ta ‘yan adawa lamarin da ake ganin zai iya hana ruwa gudu wajen gudanar da mulki a kasar musamman ga sabuwar gwamnatin Nana Akufo Addo da ‘yan adawan suke zargin da bai lashe zaben bisa ka’ida ba.

Sai dai kuma masu sanya ido na kasa da kasa suna ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da kuma daidai da doka duk kuwa da ‘yan wasu abubuwa da suka faru wadanda ba za su iya sanya alamun tambaya kan ingancin zaben ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!