PEC : ‘Yan jarida 600 Cutar Covid-19 Ta Kashe a Duniya

2021-01-07 10:10:22
 PEC : ‘Yan jarida 600 Cutar Covid-19 Ta Kashe a Duniya

Wata kungiya mai zaman kanta dake tattara alkaluman ‘yan jaridun da suka mutu a sassan duniya, ta ce sama da ‘yan jarida 600 annobar korona ta kashe daga watan Maris na 2020, zuwa karshen shekarar.

Kungiyar mai suna PEC a takaice tace daga cikin jumillar ‘yan jaridu 602 da annobar ta korona ta kashe, 303 sun mutu ne a yankin Latin ko Kudancin Amurka, 145 a Asiya, 94 a Turai, 32 a Amurka, sai kuma nahiyar Afrika da cutar ta kashe 28.

Sai dai rahoton kungiyar sa idon ta PEC yace ba zai yiwuwa a iya tantance manema labaran da suka mutu suna kan aiki ba.

Kungiyar ta bukaci a sanya ‘yan jarida a cikin mutanen dake sahun gaba cikin masu bukatar a yi musu allurar riga kafin cutar korona bisa bukatarsu.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!