FAO : Barazanar Farin Dango A Habasha Da Kenya Za Ta Yi Muni

2021-01-05 09:54:42
FAO : Barazanar Farin Dango A Habasha Da Kenya Za Ta Yi Muni

Hukumar kula da abinci da ayyukan gona ta MDD, cewa da FAO, ta yi gargadin cewa, za a samu farin dango masu yawan gaske da za su watsu a kudancin kasar Habasha da wasu sassan kasar Kenya a wannan wata na Janairu.

A cewar hukumar FAO, akwai tarin farin dango da suka kyankyashe a gabashin kasar Habasha da tsakiyar Somalia, wadanda suka nausa zuwa yankunan kudancin Habasha, wanda kuma sun riga sun isa arewacin Kenya a ranar 21 ga watan Disamba.

An gudanar da gagarumin aikin dakile farin dangon a gonakin da suka zarce hekta dubu 336 a watan Disamba, kuma za a ci gaba da kiyaye matakan.

Tun a watan Yunin shekarar 2019, Habasha take fama da mummunar barnar farin dango wanda ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 25, inda suka haifar da babbar illa ga amfanin gona a sassan kasar.

Farin dango dai sun kasance a matsayin babbar barazana ga shirin samar da abinci a yankuna masu hamada da ya shafi kasashen duniya 20, wanda ya fara tun daga yammacin Afrika har zuwa Indiya, wanda ya shafi filayen noma da suka kai kilomita miliyan 16, kamar yadda MDD ta bayyana.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!