Iran: An Fara Aikin Tace Sanadarin Uranium Zuwa Kashi 20% A Cibiyar Fordow

2021-01-04 21:40:17
Iran: An Fara Aikin Tace Sanadarin Uranium Zuwa Kashi 20% A Cibiyar Fordow

Kakakin fadar shugaban kasa a nan Iran ya bada sanarwan cewa an fara gasa sinadarin uraniyom zuwa kashi 20% a cibiyar makamashin nukliya ta Fordow dake kudancin Tehran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ali Rabi’ii yana fadar haka a safiyar yau Litinin, Ya kuma kara da cewa an fara aikin ne tare da umurnin shugaban kasa, don yin aiki da kudurin majalisar dokokin kasar wanda ya bukaci hakan, a matsayin daya daga cikin matakan da kasar take dauka don ganin an dauke mata takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa mata.

Rabi’ii ya kara da cewa a yau Litinin ce za’a fara samun sinadarin uraniyom wanda aka gasa zuwa kashi 20% . Kuma an fara aikin ne baya sanarda hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA da kuma gabatar mata yadda tsarin gasawar zata kasance. Iran ta yi amfani da sabbin na’urorin gasa uraniyom samfurin IR6, UF6 da kuma IR2M a aikin gasawar.

019

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!