​Zidane: Real Madrid Ta Fara Tabuka Abin A Zo A Gani

2020-12-26 18:28:03
​Zidane: Real Madrid Ta Fara Tabuka Abin A Zo A Gani

Zinadine Zidane, mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ya bayyana cewa, kokarin ‘yan wasan kungiyar ya fara dawowa bayan nasarar da suka samu a ranar Larabar akan kungiyar Granada a gasar La liga.

Tun farko dai Real Madrid ta bayyana ‘yan wasanni 24 da za su fuskanci Granada a wasan cin kofin La Ligar na ranar Laraba, cikinsu har da Eden Hazard saboda rabon da dan kwallon tawagar Belgium din ya buga wa kungiyar wasa tun raunin da ya yi a karawa da Alabes ranar 28 ga watan Nuwamba.

Hazard dai na fama da yawan yin raunin tun bayan da ya koma Real Madrid da buga wasa daga Chelsea sannan sauran ‘yan wasan da suka fafata da Granada har da Isco da kuma Binicius Junior.

Sai dai Real Madrid ta buga karawar ta ranar Laraba ba tare da dan wasa Luca Modric ba, wanda ya yi rauni a wasan da sukayi nasara a kan Eibar da ci 3-1 ranar Lahadi kuma kawo yanzu Real Madrid tana mataki na biyu a teburi da tazarar maki iri daya tsakaninta da Atletico Madrid mai jan ragama ita kuwa Granada tana matsayi na bakwai da makinta 21.

Dan wasa Casemiro ne ya fara zurawa kungiyar ta kasar Sipaniya kwallonta ta farko a raga kafin daga baya kuma Karim Benzema, wanda a satin daya gabata Zidane ya ce babu kamarsa a kungiyar ya jefa kwallo ta biyu.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!