Shamkhani: Babu Makawa Iran Za Ta Dauki Fansa A Kan Kisan Qasem Sulaminai

Babban sakataren majalisar tsaron
kasa a Iran ya bayyana cewa, babu makawa kasar za ta dauki fansa a kan kisan
Qasem Sulaimani.
Babban sakataren majalisar tsaron
kasa a Iran Admiral Ali Shamkhani ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake ganawa da babban mai bawa
shugaban kasar Afghanistan shawara kan harkokin tsaro Hamdallah Muhib a birnin
Tehran.
Ya ci gaba da cewa, matakin daukar
fansa da Iran za ta dauka kuwa zai shafi wadanda suka bayar da umarnin yin
kisan ne, da kuma wadanda suke da hannu wajen aiwatar da kisan.
Dangane da alaka tsakanin kasashen
Iran da Afghanistan kuwa, Shamkhani ya bayyana cewa, alaka ce ta tarihi da
addini da kuma al’adu da kuma makwabtaka, wadda kuma alaka ce tabbatatta wadda
babu abin da zai iya girgiza ta.
Ya kara da cewa, har kullum burin
Iran shi ne ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a kasar Afghansitan, da kuma samun hadin kai
da fahimtar juna da sulhu tsakanin dukkanin bangarori na al’ummar kasar.
A nasa bangaren babban mai bawa
shugaban kasar Afghanistan shawara kan harkokin tsaro Hamdallah Muhib ya
bayyana cewa, a kowane lokaci za su ci gab da kasancewa tare da kasar Iran da
kuma karbar shawarwarinta, kamar yadda kuma za su ci gaba da kara karfafa alaka
da bunkasa ta tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
015