A Falastinu An Fatattaki Wasu Larabawan Yankin Gulf Masu Yawan Shakawata A Isra’ila

Falastinawa sun nuna fushinsua kan wasu larabawan Bahrain da hadaddiyar daular larabawa da suka
ziyarci Isra’ila domin yawon shakatawa.
Jaridar ra’yul yaum ta bayar rahoton
cewa, larabawan wadanda suka shiga cikin yankunan Falastinawa da visa ta
Isra’ila, sun gamu da fushin al’ummar Falastinu, inda ake jefe su da takalma da
kuma yi musu eho a duk inda suka shiga cikin yankunan Falastinawa.
Rahoton ya ce, larabawan na Bahrain
da hadaddiyar daular larabawa sun shiga cikin harabar masallacin Quds, amma masu kula da masallacin
suka hana su shiga, daga karshe dai sun shiga masallain mai alfarma ta kofar da
yahudawa suke shiga
Wani daga cikin yahudawa masu
tsatsauran ra’ayi ya bayyana wa tashar talabijin ta 11 ta Isra’ila cewa, ya yi
mamakin yadda Falastinawa suka hana larabawan Bahrain da na hadaddiyar daular larabawa shiga cikin
masallacin quds, wanda hakan ke nuni da cewa Falastinawa ba su yarda da kulla
alaka da Isra’ila da gwamnatocin wadannan kasashe suka yi ba.
Ya kara da cewa, yahudawa ne suka
baiwa larabawan ‘yan yawan shakatawa a Isra’ila kariya, domin kare su daga abin
da ka iya faruwa da su, sakamakon fushin da Falastinawa suka nuna dangane da
zuwan nasu karkashin Bakunin yahuwan Isra’ila.
015