Adadin Mutanen Da Suke Ci Gaba Da Kamuwa Da Korona Yana Raguwa A Iran

2020-12-19 20:10:26
Adadin Mutanen Da Suke Ci Gaba Da Kamuwa Da Korona Yana Raguwa A Iran

Mai Magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran, Sima Sadat Lary ta fada a yau Asabar cewa; A cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin wadanda su ka kamu da cutar su ne dubu 6 da 421, wadanda kuma aka kwantar a asibiti su ne; 822.

Danagne da wadanda su ka rasa rayukansu a cikin sa’o’i 24 da suka gabata kuwa, mai Magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran din ta ce; sun kai 175.

Wannan adadin ma wadanda suke kamuwa da kuma mutuwa daga cutar ta corona a Iran ya ragu matuka idan aka kwatanta da makwanni uku da su ka gabata, inda fiye da mutan dubu 10 su ke kamuwa da ita, wadanda kuma suke mutuwa suke karatar 500 a kowace rana.

Iran din dai tana cikin kasashen da suke kokarin samar da allurar riga-kafin cutar ta corona, inda a halin yanzu aka shiga cikin fagen yin gwaji ga mutane.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!