Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar Ghana Sun Raba Kusan Dukkanin Kujerun Majalisar Dokokin Kasar A Tsakaninsu

2020-12-15 15:03:19
Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar Ghana Sun Raba  Kusan Dukkanin Kujerun Majalisar Dokokin Kasar A Tsakaninsu

Jam’iyyar NPP mai mulki ta lashe kujeru 137 daga jumillar kujeru 273 da ake da su a majalisar dokokin kasar, yayin da jam’iyyar adawa ta NDC ta samu kujeru 136.

Kujera daya da ta rage, wani dan takara ne mai zaman kansa Andrew Amoako Asiamah daga mazabar Fomena ya lashe ta.

Hukumar zaben kasar ce ta sanar da wannan sakamakon na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar a ranar Litinin din da ta gabata.

A makon da ya shude ne dai aka yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalsiar dokokin kasar ta Ghana, inda muhimman ‘yan takarar biyu, wato shugaba mai ci Nana Akufo Addo da kuma tsaohon shugaban kasa, John Drama Mahama su ka yi karo da juna.

Shugaban kasar mai ci ya lashe zaben, ba da wata tazara mai yawa ba.

Kasar Gahna dai tana cikin tsirarun kasashen nahiyar Afrika da ake yabawa a fagen tsarin demokradiyya.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!