Daliban Da Aka Sace A Makarantar Kwana Da Ke Kankara A Jihar Katsina A Nigeria Sun Kai Daruruwa

2020-12-14 10:01:56
Daliban Da Aka Sace A Makarantar Kwana Da Ke Kankara A Jihar Katsina A Nigeria Sun Kai Daruruwa

Majiyar ‘yan sanda ta sanar da cewa; Wasu mutane ne dauke da bindigogin Ak-47 su ka kutsa makarantar kwana dake Kankara da misalin karfe 9;40 inda su ka yi awon gaba da dalibai.

Harin dai ya zo ne a lokacin da shugaban kasar Muhamamdu Buhari yake ziyara a mahaifarsa ta Daura da ke jihar ta katsina.

Har zuwa yanzu dai jami’an tsaro suna bincike domin gano adadin daliban da aka yi awon gaba da su.

Wannan harin na ‘yan bindiga yana daga cikin mafi muni da aka kai a wata makarantar kwana, tun bayan harin da aka kai a garurun Dapchi a 2018 da kuma na Chibok a 2014 a yankin arewa maso gabashin kasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!