Najeriya: Za A Kara Kudin Wutar Lantarki A Farkon Watan Yuli

2020-06-29 14:55:24

Gamayyar

kamfanonin rarraba wutan lantarki a tarayyar Najeriya (DisCos) ta bada sanarwan

cewa za’a fara aiwatar da Karin da aka yiwa wutan lantarki a kasar daga ranar

daya ga watan Yili mai zuwa.

Jaridar “Premium Times” ta Najeriya ta nakalto Sunday Oduntan lauyan kungiyar ta (DisCos) yana fadar haka a jiya Lahadi a Abuja. Ya kuma kara da cewa gwamnatin Najeriya ta yi kokarin janye kanta daga batun Karin farashin wutan, amma kuma tare da ita aka amince da yin Karin.

Labarin ya kara da cewa za’a kara farashin wutan da kasha 60 a wurare kamar Ikeja na jihar Legos sannan da kasha 73 a Abuja sai kuma kasha 78% a Enugu. Kamfanin DisCos ya kara da cewa an dauki wannan matakin ne don jawo masu zuba jari a cikin harkar samarwa da kuma rarraba wutan lantaki a kasar.

Sai dai mutanen kasar suna korafin cewa har yanzun wutan bata tsaya ba, don haka bai kamata a ce an kara farashinsa ba.

Tags:
Comments(0)