​Najeriya: Adadin Wadanda Suka Rasu Sakamakon Kamuwa Da Corona Ya Kai 200

2020-05-21 17:10:00

Rahotanni da cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta fitar, ya nuna cewa adadin wadanda suka harbu da cutar Covid -19 a Najeriya ya kai 6677, bayan da aka samu mutane 284 da suka kamu da cutar a jiya Laraba, inda ya zuwa yanzu mutane 200 ne aka tabbatar da sun rasa rasa rayukansu a fadin kasar, sakamakon kamuwa da wannan cuta.

Jihar legas ce ke da kaso mafi yawa na dadin wadanda suka kara harbuwa da cutar. A yanzu haka dai kimanin mutane 1840 ne aka sallama daga wajen da ake killace da su bayan da suka suka warke.

Karamin Minsitan lafiya na Najeriya ya nuna jin dadinsa game da kokarin da aka yi na samar da cibiyoyin gwajin mutane masu dauke da cutar ta Korona a dukkanin jihohin kasar.

A gefe guda kuma babban sufeto janar na ‘yan sanda na kasa Muhammad Adamu ya umarci jami’an ‘yan sanda da su aiki da nuyin da ke kansu a daidai lokacin da likitoti ke yajin aiki a jihar Lagos.


Tags:
Comments(0)