​China Ta Caccaki Amurka Game Da Saka Wa Kamfaninta Takunkumi

2020-05-21 16:51:22

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Zhao Lijian ya fadi cewa, matakin da ma’aikatar baitul malin kasar Amurka ta dauka na kakaba wa kamfanin China na Shangai Saint Logistic takunkumi, saboda zarginsa da yin alaka da Iran, hakan ya sabawa doka.

Ita dai Amurka ta zargin kamfanin ne da taka rawa a madadin kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Mahan mallakin kasar Iran.

Har ila yau ya kara da cewa kowace kasa tana da ‘yanci kamar yadda dokokin kasa da kasa suka bata na yin hulda, ko kuma kulla dangantaka ko wata yarjejeniya tsakaninta da kasar Iran, babu wata doka ta duniya da ta hana yin hakan.

Kasar Amurka ta sanya sunan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Mahan na kasar Iran cikin kamfanonin da ta haramta yin mu’amala da su, bayan da ta zargi kamfanin da yin aiki tare da dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran.

Amurka ta matsa lamba kan wasu kasashe da su sanya wa kamfanin na Mahan takunkumi ko kuma su soke hakkin yin zirga-zirgarsa a cikin kasashensu, amma kasashe da dama sun yi watsi da bukatar ta Amurka, daga ciki hard a kasashen China da Rasha.

Tags:
Comments(0)