Zanga zangar Goyan Bayan Falasdinu A Yayin Bude Taron Kolin G7

An fara taron koli na kwanaki uku na kungiyar G7 na shekara ta 2024 a cikin zanga-zanga, a Borgo Egnazia, wani wurin shakatawa dake kusa

An fara taron koli na kwanaki uku na kungiyar G7 na shekara ta 2024 a cikin zanga-zanga, a Borgo Egnazia, wani wurin shakatawa dake kusa da garin Fasano a kudancin yankin Apulia na kasar Italiya.

Rikicin Ukraine da na Gabas ta Tsakiya da kuma dangantakar dake tsakanin kungiyar da kasashe masu tasowa su ne batutuwan da aka mai da hankali a kai cikin ajandar taron.

Kana za a tattauna gudanar harkokin kirkirarriyar basira wato AI, da batutuwan da Afirka take fuskanta da sauyin yanayi a yayin taron.

A ranar bude taron, a Brindisi, masu zanga-zanga sun rike tutocin Falasdinu tare da daga kwalaye masu dauke da taken “Kauracewa G7,” “Dakatar da Rusa Duniya”, da “A Daina Yaki”.

Sun soki kungiyar G7 da gaza taka rawar gani wajen kare muhalli, adalci da zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments