A jawabinsa na farko bayan zabensa a matsayin Sabon babban sakataren Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem, ya bayyana cewa, kungiyar za ta ci gaba da gwagwarmaya domin dakile makircin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a kan daukacin yankin gabas ta tsakiya.
Sheikh Naim Qassem ya yi gargadin cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da masu goyon bayanta na yammacin Turai suna cikin wannan babban makirci da ake kitsawa yankin.
A jawabinsa na farko da aka watsa ta gidajen talabijin da dama a kasashen duniya a wannan Laraba, ya bayyana cewa, shirinsa na zahiri shi ne ci gaba da ayyukan marigayi Sayyid Hassan Nasrallah.
“Za mu ci gaba da aiwatar da shirin yaki wanda Sayyed Nasrallah ya tsara, kuma za mu ci gaba da kasancewa a kan turba ta siyasa daidai da manufofin kungiyar.”
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya jaddada cewa goyon bayan Gaza yana da matukar muhimmanci wajen tinkarar hatsarin gwamnatin sahyoniya a yankin baki daya.
An kafa kungiyar Hizbullah ne a shekara ta 1982 domin tunkarar mamayar Isra’ila da manufar fadadarta da kuma ‘yantar da kasar Lebanon da ta mamaye, in ji Sheikh Qassem.
Ya kuma yi tsokaci kan sukar da ake yi cewa gwagwarmayar Gaza da Lebanon ne ya tunzura Isra’ila take aikata kisan kiyashin da take yi.
Ya ce : kada jama’a su manta da ta’asar da Isra’ila ta yi na tsawon shekaru 75, da kuma rawar da kungiyyoyin gwagwarmaya suka taka wajen kawo karshen mamayar haramtacciyar kasar kasar Labanon.
“Wasu suna yayata cewa an tsokani Isra’ila, amma Isra’ila na bukatar hujja ne kafin ta aiwatar da ta’addanci? Shin mun manta shekaru 75 ana kashe Falasdinawa, da murkushe su, da kwace musu kasa, da kwace wurare masu tsarki da keta alfarmarsu da kuma kisan kiyashi da Isra’ila ta yi a cikin tsawon wadannan shekaru? Shi ma an tsokane ta ne?
Gwagwarmaya ce ta kori Isra’ila daga kasarmu, tare da hadin gwiwar sojoji da jama’ar kasa, amma Kudirin majalisar dinkin duniya bai kori Isra’ila daga kasar Lebanon ba.” in ji sheikh Na’im Qassem.
Sheikh Qassem ya ce Benjamin Netanyahu da kansa ya bayyana a farkon harin da Isra’ila ta kai wa Labanon cewa ta yi hakan ne dominabin day a kira “Sabuwar Gabas ta Tsakiya”.
“Muna fuskantar gagarumar barazana a yankin gabas ta tsakiya ; wannan yaki ne da ya wuce Lebanon da Gaza; yaki ne da yashafi duniya.”
“Ana amfani da duk wani nau’i na zalunci domin kawar da al’ummar Falastinu da kawar da duk wani yunkuri na kin mika wuya ga wannan zalunci da kuma duk wani mai goyon bayan Falastinu da hakkokinsu, a kan haka dole ne mu fuskanci wannan zalunci maimakon tsayawa muna kallo.”
Shugaban na Hizbullah ya ce wannan arangama ta zubar da mutuncin kasashen yammacin duniya bisa la’akari da son zuciya da suke nuna karara ba tare da wata kunya ba akan ayyukan dabbancin da Isra’ila take aikatawa a yankin.
Shugaban na Hizbullah ya jaddada cewa gwagwarmayar da ake yi a yankin na fafutukar ganin an samu makoma mai daraja ita kadai ce mafita, domin kuwa nuna tsoro da mika wuya ga yahudawan sahyuniya, babu abin da zai haifarwa masu yin haka illa kaskanci da wulakanci da tozarta, kuma basu taba burge yahudawan sahyuniya ba.
“Tsarin gwagwarmaya da tsayin daka a Gaza da Lebanon wani almara ne na kare mutunci da karama ga dukkanin al’ummomin yankin gabas ta tsakiya da makomarsu.”
Sheikh Qassem ya fayyace cewa kungiyar Hizbullah ba ta yaki a madadin ko wane bangare, amma tana kare kasar Lebanon da al’ummarta da mutuncinta.
Ya kuma yaba da goyon bayan Iran take baiwa dukkanin kungiyoyi gwagwarmaya da zaluncin yahudawan Haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin, ba ta taba neman wani abu na taimako daga gare su a madadin hakan ba, in ji Sheikh Qassem.
“Iran ta fahimci irin girman sadaukarwar da take yi wajen taimakon lamarin Falastinu, babban misalign hakan shi ne yadda ta rasa manyan kwamandojinta na soji, da suka hada hard a Janar Qassem Sulaimani.
“Muna yaki a kasarmu kuma muna kokarin kwato yankinmu da aka mamaye; ba wanda ya tambaye mu wani abu, kuma ba wanda ya dora mana komai na daga sharadda .”
Sheikh Qassem ya godewa majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah da ta zabe shi a matsayin shugaban kungiyar, yana mai kallon wannan matakin a matsayin wata babbar amana da aka dora a kan wuyansa.
Wannan amana ta samo asali ne daga kalaman Sayyed Abbas al-Musawi (shugaban Hizbullah na farko) cewa: ‘Babban umarni na wannan amana shi ne kiyaye tsayin daka da gwagwarmaya.
Sheikh Qassem ya yi ta’aziyyar shahadar Sayyed Hashem Saffieddine, shugaban majalisar zartarwa ta Hizbullah. Ya bayyana Sayyed Saffieddine a matsayin mutum “mai tsari” wanda ya ci gaba da aiki bisa himma da kwazo na tsawon lokacin rayuwarsa ta gwagwarmaya, yana da hangen nesa, kula da mayaka da dai sauran ayyuka da ya yi da suke tabbatar da matsayinsa na babban gwarzo dab a za a manta da shi a tafarkin gwawarmaya ba.
“Ya kasance daya daga cikin fitattun mutanen da Sayyed Hassan Nasrallah ya dogara da su wajen aiwatarwa da kuam zartar da manufofi na kungiyar Hizbullah.”
Sheikh Qassem ya kuma yi ta’aziyyar shahadar shugaban Hamas Yahya Sinwar, yana mai bayyana shi a matsayin “samfuri na jarumtaka da tsayin daka” na Falasdinu da gwagwarmaya ta ‘yantattu a duniya.
“Ya yi shahada yayin da yake yaki har zuwa numfashinsa na karshe, jarumi, mai aminci, mai gaskiya, mai daraja, wanda ya fifita shahada a kan rayuwa c ikin kaskanci da mika wuya ga sahyuniyawa.”
Dangane da Sayyid Hassan Nasrallah kuwa, Nasrallah, Sheikh Qassem ya ce, shi ne mai dauke da tutar gwagwarmaya da zaluncin yahudawa da masu girman kai, kuma tutarsa za ta ci gaba da kadawa har zuwa samun nasara da yardarm Allah madaukakin sarki.