Yemen : ‘Yan Houthi Sun Kai Hari Kan Jiragen Ruwan Isra’ila, Amurka, Da Burtaniya A Teku

Kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a kasar Yemen ta sanar cewa ta kaddamar da sabbin hare haren soji kan jiragen

Kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a kasar Yemen ta sanar cewa ta kaddamar da sabbin hare haren soji kan jiragen ruwa a Bahar Maliya, da tekun Arabian da Bahar Rum da Tekun Indian Ocean, a matsayin ci gaba da nuna goyan baya ga Falasdinawa a Gaza dake fuskantar hare haren Isra’ila.

A wata sanarwa, kakakin sojin kungiyar, Yahya Saree ya ce mayakansu sun hari jiragen ruwa “masu alaka da Isra’ila, Amurka, Burtaniya da Isra’ila” ta amfani da makamai masu linzami kuma harin ya yi nasarar kai wa ga jiragen.

Sanarwar ta yi nuni da cewa kungiyar ta kai hari kan jirgin ruwan Isra’ila MSC Unific a tekun Arabian Sea, da jirgin dakon mai na Amurka Delonix, a Bahar Maliya, da jirgin Burtaniya “Anvil Point”, a tekun Indian Ocean, da jirgin Lucky Sailor, a Bahar Rum, ba tare da fayyace kasar da abin ya shafa ba.

Dakarun Yeman din sun sha alwashin ba za su daina ba, matukar ba a daina kai hare-hare Gaza ba tare da dage killacewar da akayi wa yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments