Yemen: Wuce Gona Da Irin HKI Ba Zai Sauya Mana Ra’ayi Akan Ci Gaba Da Taimaka Wa Gaza Ba

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa  ita

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa  ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.”

Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa;  Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai yi tasiri akan matsayarmu ta taimakawa Gaza ba,sannan kuma ya kara da cewa; Abinda Isra’ila makiya ke son yi, shi ne a kyale ta yi yadda take so da Falasdinawa ba tare da an mayar mata da martani ba daga kowace kasa ta musulmi.”

Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Matsayar da kasar Yemen take dauka na taimakawa Falasdinawa, matsaya ce ta addini.”

Haka nan kuma ya kara da cewa; Daga cikin manufofin harin na Isra’ila a filin saukar jiragen sama na Sanaa da akwai dakatar da jigilar mahajjata, amma ba za su yi nasara ba.”

Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya yi ishara da wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki,sannan kuma ya ce; A wannan lokacin wahalhalun na mutanen Falasdinu sun fi na baya, domin suna fuskantar yunwa da kuma ci gaba da kai hare-hare da Isra’ila take yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments