Yemen Tana Bukukuwan Samun Nasara Kan Amurka Kuma Zata Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Gaza

Dubban daruruwan mutane a kasar Yemen sun fito kan tituna suna bayyana jin dadinsu da samun nasara a kan kasar Amurka a yakin da suka

Dubban daruruwan mutane a kasar Yemen sun fito kan tituna suna bayyana jin dadinsu da samun nasara a kan kasar Amurka a yakin da suka dau makokinni suka fafatawa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an daw makonni jiragen yakin Amurka suna kai hare-hare kan wurare daban daban a kasar Yemen da sunan tilastawa kasar dakatar da kaiwa jiragen ruwan Amurka da kuma na HKI wucewa da tekun Red sea don tallafawa mutanen Gaza, wadanda HKI take masu kissan kare dangi da kuma hana shigar abinda zuwa cikin gaza don kashesu da yunwa.

A ranar Laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fito ya fadawa duniya kan cewa, ya cimma yarjeniya da kasar Yemenkan cewa ba zasu sake kaiwa jiragen ruwan Amurka hare-hare a tekun Maliya ba. Don haka ita ma Amurka zata janye daga tekun red sea tare da kawo karshen yaki da mutanen kasar Yemen.

Majiyar gwamnatin ceto ta kasar Yemen ta ce ta yarda da matakin da Amurka ta dauka, amma kuma hare-hare a kan HKI zasu ci gaba har zuwa lokacinda zata dakatar da hare-hare a kan Falasdinawa a Gaza da kuma bude hanya don shigar abinda da kuma bukatun Falasdinawa a gaza.

Sai dai majiyar da gwamnatin kasar Yemen tace idan Amurka ta sake kaiwa mutanen kasar Yemen suma zasu dawo da kai mata hare-hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments