Yemen Ta Yi Kira Ga Saudia Ta Kawo Karshen Yaki Da Ita

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Yemen ta yi kira ga gwamnatin kasar Saudia ta tabbatar da gaskiyar abinda ke faruwa a kasa a yakin da take

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Yemen ta yi kira ga gwamnatin kasar Saudia ta tabbatar da gaskiyar abinda ke faruwa a kasa a yakin da take fafatwa da sojojin kasar, musamman a kuduncin kasar, na faduwa daya bayan daya. Ta kuma kawo karshen yakinda take yi a kudancin kasar wanda babu nasara.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen ta kasar Yemen na fadar haka a jiya Talata, ta kuma kara da cewa, babu nasarar da sojojin Saudia da sojojin hayarta suke samu a kasar don haka abinda ya fiye masu shi ne su kawo karshen yakin sun kuma zauna kan teburin tattaunawa don warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar lumani.

Daga karshe bayanin yakara da cewa a halin yanzu kasar Yemen yentacciyar kasashen wacce ba zata taba amincewa da bauta ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted