Shugaban mujallar Sabaa ta kasar Yemen ya bayyana cewa, nasarar da dakarun kasar Yemen suka samu a kan saudia da kawayenta a kubutar da yankunan bakin ruwa na Tekun Aden ya zowa makiya da mamaki, amma nasarar ba shirin yau bane. Saboda sojojin San’aa sun yiwa yakin da ya kwato wadannan yankuna shiri , muna iya cew na shekaru 8 da suka gabata.
Tashar talabijan ta Al-masira ta kungiyar Ansarallah, ta kasar Yemen ta nakalto Nasruddeen Aamir shugaban Mujallar Sabaa yana fadar haka a hari ta musamman da ta hada shi da shi.
Aamir ya ce, dakarun Yemen sun yi shiri sun kuma yi hakuri, sun kuma tsara dabarbaru masu inganci, wadanda suka bata shirin Saudia, Burtania, Amurka da HKI na sake maida ikonsu a kan mashigar ruwa ta babul mandab.
Aamir ya taya shugaban kungiyar Ansarallah na kasar ta Yemen Sayyed Abdulmalik Badruddeen Huthi, da shugaban majalisar siyasa ta kasar Yemen Mahdi Almashd, da sojojin kasar da kuma sauran mutanen kasar Yemen kan wadan nan nasarori daya bayan daya.
Yace duk tare da tallafin da sojojin Saudia suka samu daga Amurka da Burtania da HKI sun kasa samun nasara a kan sojojin kasar Yemen, kuma godiya da yabo sun tabbata ga All..kuma shine mai bada nasara.