Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a tarayyar Najeriya sanadiyyar tumutsitsi a wasu wuraren raba abinci da kayakin kirsimeta ya karu zuwa 32.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa mutanen 22 suka mutu a turmutsitsin da aka samu a garin Okiji na jihar Anambra a lokacinda wani coci ya bude kofarta don rabawa mutane abinci da kayakin kirsimeti.
Haka ma a birnin Abuja irinsa ya auku inda aka tattaka wasu mutane bayan sun fadi kasa a lokacinda aka bude kofar wani coci don raba abinci da kayakin kirsimeti a garesu kyauta.