Search
Close this search box.

Yawan Shahidan Yan Jarida A Gaza Suna Kara Yawa Tare Da Wadanda Suka Yi Shahada A Baya Bayan Nan

Ofishin kafafen yada labarai na kasar Falasdinu a Gaza, ya bada sanarwan cewa yawan yan jaridu da suka yi shahada ya karu zuwa 169 daga

Ofishin kafafen yada labarai na kasar Falasdinu a Gaza, ya bada sanarwan cewa yawan yan jaridu da suka yi shahada ya karu zuwa 169 daga farkon yakin Tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto ofishin kafafen yada labaran na Falasdinawa a Gaza na yin allawadai da kissan yan jaridu wanda HKI take yi a Gaza, kuma ya  dorawa HKI laifuffukan kissan yan jaridu a cikin watanni 10 da suka gabata a Gaza.

Hukumar kafafen yada labaran ya yi kira ga kungiyoyin kare hakkin bil’adama da kuma wadanda abin ya shafa da su takawa HKI birika a kan irin yadda take kissan yan jarida a Gaza.

Hukumar bada agaji ta MDD ta musamman a kasar Falasdinawa, UNRWA ta bada sanarwan cewa jami’an bada agaji 289 ne sojojin HKI suka kashe a Gaza tun farkon yakin, watanni kimani 10 da suka gabata.

Hukumar UNRWA ta kara da cewa 207 daga cikinsu ma’aikatar hukumar ce. Sannan yahudawan sun kashe jami’an jinya wadanda suka hada da ikitoci, mataimakan likitoci har  889 a yakin.  Ibrahim Maharin shi ne dan jarida na karshe wanda sojojin HKI suka kashe a garin Khan Yunus na yankin Gaza.

Ya zuwa yanzu dai ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza sun bada sanarwan cewa sojojin HKI sun kashe mutane fiye da dubu 40 a gaza sannan wasu fiye da dubu 92 suka ji rauni, a yayinsa wasu dubu 10 suka bace ko ba’a san inda suke ba tun bayan fara yakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments