Yawan Marasa Gidaje A Amurka Ya Karu Da Kashi 10%

Pars Today- Bisa ga kididdigar kwanan nan, rashin matsuguni ya zama babbar matsala a duk faɗin Amurka. Kididdigar shekara-shekara da aka tattara daga yankuna daban-daban

Pars Today- Bisa ga kididdigar kwanan nan, rashin matsuguni ya zama babbar matsala a duk faɗin Amurka.

Kididdigar shekara-shekara da aka tattara daga yankuna daban-daban na birane da karkara sun nuna karuwar marasa gida a fadin Amurka. A cewar Pars Today, jaridar Wall Street Journal ta sanar da cewa karuwar rashin matsuguni a kasar na nufin cewa watakila Amurka za ta zarce adadin marasa matsuguni 653,000 a shekarar 2023, adadi mafi girma tun shekarar 2007.

A cewar Wall Street Journal, fiye da kungiyoyi 250 da ke tallafawa marasa gida a Amurka, sun yi rajistar ƙididdiga na akalla 550,000 marasa matsuguni a rana ɗaya a farkon 2024. Wannan yana nuna haɓaka 10% idan aka kwatanta da bara.

Ƙididdiga ta ƙarshe na marasa matsuguni a Amurka ya dogara da tarin alkaluman yankuna kamar birnin New York wanda ke da mafi yawan marasa matsuguni a tsakanin sauran biranen.

Jaridar Wall Street Journal ta sake nanata cewa ba bakin haure ne kawai ke kara yawan marasa matsuguni a Amurka ba, a’a, rage tallafin kudi, karin farashin gidaje da haya ne ya tilastawa mutane barin gidajensu don zama a tituna.

A cewar wannan rahoto, ana iya ambaton rikicin lafiyar hankali da kuma shan muggan ƙwayoyi a matsayin dalilin da zai ƙara rashin matsuguni a Amurka. A bara, Amurka ta yi rajistar wani sabon tarihi a fannin rashin matsuguni na yau da kullun wanda ya haɗa da naƙasassu waɗanda koyaushe ba su da matsuguni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments