Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Sun Kai 45,259 Tun farkon Fara Kai Hari Kan Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aikata muggan laifuka da kisan kare dangi kan Falasdinawa a rana ta 444 a jere Hare-haren wuce gona

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aikata muggan laifuka da kisan kare dangi kan Falasdinawa a rana ta 444 a jere

Hare-haren wuce gona da iri da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suke kai wa Zirin Gaza suka shiga kwana na 444 a jere a safiyar yau Litinin, wanda suke aiwatar da kisan kiyashi kan iyalan Falasdinawa da ‘yan gudun hijira tare da kai hare-hare kan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya musamman kan shiyar arewacin Zirin na Gaza.

Kafar watsa labaran Falasdinawa ta hanyar yanar gizo na cewa: Majiyoyin kiwon lafiya na Falasdinu sun bayyana cewa, Falasdinawa 50 ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu da dama a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna a Zirin Gaza tun daga wayewar ranar Lahadi zuwa yau Litinin.

Yayin da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan Zirin Gaza ya haura zuwa shahidai 45,259, baya ga 107,627 da suka jikkata tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 miladiyya.

A cewar ma’aikatara lafiyar, ayarin sojojin mamayar Isra’ila sun bude wuta sosai kan asibitin Kamal Adwan da ke aikin yankin Beit Lahiya a arewacin Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments