Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimani yara 3,500 suka rasa rayukansu a kokarin ketara tekun Medeteranina a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Spunic na kasar Rasha ya nakalto hukumar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan.
Labarin ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa akalla yaro guda ne ya ransa ransa a ko wace rana. Kuma kashi 7/10 daga cikinsu sun halaka ko sun bace ne su kai ba ba tare da rakiyar iyayensu ba. Har’ila yau rahoton ya kara da cewa akalla mutane 20,803 suka halaka a tsakiyar tekun na Mediterranean a kokarinsu na tsallakawa zuwa kasashen na turai.
Daga karshe hukumar tace ba za’a iya sanin hakikanin adadin wadanda suka halaka ba saboda a cikin wasu kwale-kwalen babu wanda ya rayuwa da za’a sami labara daga wajensa ba.