Yara A Karon Farko Sun Fara Shan Riga Kafin Cutar Shan Inna A Gaza Tun Bayan Fara Yaki Watanni Kimani 11 Da Suka Gabata

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bada sanarwan cewa daga yau lahadi ce ake saran ma’aikatar hukumar zata fara yiwa yara yan kasa da shekaru

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bada sanarwan cewa daga yau lahadi ce ake saran ma’aikatar hukumar zata fara yiwa yara yan kasa da shekaru 5 riga kafin cutar shan Inna a zirin Gaza, banda haka tana saran kafin wa’adin da HKI ta bayar za’a yiwa ko shayarda yara 640,000 maganin riga kafin cutar a duk fadin zirin Gaza.

Hukumomi a Gaza dai sun bayyana cewa za’a gudanar da aikin riga kafin cutar ta poliyo ne a asbitin Nasir dake tsakiyar Gaza, kuma za’a bi sauran sansanonin yan gudun hijira don gudanar da aikin.

Labarin ya kara da cewa gwamnatin HKI ta bada kwanaki uku kacal don yiwa yaran na Gaza maganin cutar ta shan-Inna ko Polio, sannan zata dakatar da bude wuta ne a ko wace rana daga 6 na safe zuwa 3 na yamma ne kawai, sai kuma gobe har a cika kwanaki uku.

A karon farko an gano cutar ta shan Inna a a Gaza bayan shekaru 25 da kawo karshenta a yankin. Hakan ya faru ne saboda yakin da aka fara a yankin watanni kimani 11 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments