Rundunar Basij a yankin kudu maso gabacin kasar Iran ta bada sanarwan shahadar dakarunta guda biyu a jiya Asabar.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran, ya nakalto rundunar IRGC na yankin ya na bada sanarwan shahadar Hojjatoleslam Sadeq Mahmoudi da kuma Milad Damankesh a lokacinda suke komawa gida daga wurin aiki a cikin wata mota tasu.
Labarin ya kara da cewa shahidan biyu sun hadu da ajalinsu ne a lokacinda wasu yan ta’adda suka bude wuta a kan motarsu a lokacinda suke wucewa a wata unguwa zuwa gidajensu.
Lardin Sitan Baluchistan wanda ke kan iyaka da kasar Pakistan dai ya dade yana fada da kungiyoyin yan ta’adda wadanda suke shigowa kasar daga kasar Pakistan, wadanda kuma suke samun taimako kasashe waje, musamman kasashen yamma da wasu kasashe makobta.
Wata kungiya wacce ake kira ‘Jashul Adle” ce ta saba daukar nauyin kashe mutane a yankin, fararen hula da sojoji wadanda suke taimakawa don tabbatar da zaman lafiya a yankin.