Yan siyasar Birtaniya Sun Soki Gwamnatin Kasar Game Da Fuska Biyu Kan Martanin Da  Iran Ta kai wa Isra’ila.

Rahotanni sun bayyana cewa fitattun yan siyasar kasar Birtaniya sun mayar da martani  kan sukar Iran  da pira ministan kasar yayi inda suka tamabaye shi

Rahotanni sun bayyana cewa fitattun yan siyasar kasar Birtaniya sun mayar da martani  kan sukar Iran  da pira ministan kasar yayi inda suka tamabaye shi game da dalilan da suka sa yaki yin tir da harin da Isra’ila ta fara kai wa kan ofishin jakadancin Iran A birnin Damaskas na kasar Siriya.

Idan ana iya tunawa a ranar 1 ga watan Aprilu ne Isra’ila ta kai harin ta’ddanci kan ofishin jakadancin Iran dake siriya, daya kai ga shahadar mutane 7 , jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Imam Khamena’I yace matakin na Isra’ila tamkar hari ne ga kasar Iran kuma ya jaddada cewa dole ne a ladabtar da Isra’ila kan wannan mummunar ta’asar da ta tafka.

Pira ministan birtaniya risha sunak ya fadi a wajen zaman da majalisar kasar ta gudanar cewa gwamnatinsa ba za ta sa hannu a harin da Isra’ila za ta kai wa iran ba, amma za ta kara taimaka mata sosai ta fuskar tsaro , kuma ya bukaci Iara’ila da ta kare kamewa.

Bayanan da yayi a majalisar dokokin kasar wajen maimaita matsayar kasar game da mataken da Iran ke dauka a yankin,  ya kara tuna asirin bakar siyasar fuska biyu da gwamnatin ke yi game da abin da ke faruwa a yammacin Asiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments