Yan Sahayoniya Sun Yi Furuci Da Wahalar Da Suke Sha A Yaki Da Hizbullah

Tsohon shugaban majalisar tsaron cikin gida ta HKI Yakub Amidor ya bayyana cewa; Za a dauki lokaci mai tsawo Hizbullah tana cigaba da harba makamai

Tsohon shugaban majalisar tsaron cikin gida ta HKI Yakub Amidor ya bayyana cewa; Za a dauki lokaci mai tsawo Hizbullah tana cigaba da harba makamai masu linzami, domin babu wanda ya isa ya kwace makaman Hizbullah.

A gefe daya jaridar “Isra’ila Home” ta buga wani rahoto da a ciki ta bayyana cewa, jirage maras matuki da Hizbullah take da su, ta raba jami’an tsaron HKI da bacci saboda fadawa cikin zullumi da damuwa.

Harin da Hizbullah ta kai a gidan Fira minista Benjemine Netenyahu a ranar Asabr din da ta gabata a yankin Qaisariyyah, ya dugunzuma tunanin ‘yan sahayiniya,kamar yadda ya faru da harin da su ka kai a sansanin bayar da horo na rundunar Gulani.

An shiga makwanni na uku da sojojin HKI suke kokarin  shiga cikin daya daga garuruwan kudancin Lebanon,amma har yanzu ya gagara, domin ana bugawa ne a kan iyaka da bayan gari.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments