Search
Close this search box.

‘Yan Majlisar Dokokin Amurka: Isra’ila Makamai Ya Sabawa Doka

‘Yan Majalisar dokokin Amurka 26 sun rubuta wasika zuwa ga ministan tsaron kasar Lyod Austin da kuma ministan harkokin waje Antonio Blanken da a ciki

‘Yan Majalisar dokokin Amurka 26 sun rubuta wasika zuwa ga ministan tsaron kasar Lyod Austin da kuma ministan harkokin waje Antonio Blanken da a ciki su ka bayyana cewa, Isra’ila tana karya dokoki wajen amfani da makaman kasar Amurka.

Bugu da kari ‘yan majalisar dokokin Amurkan sun kuma aike da wata wasikar zuwa shugaban hukumar leken asirin kasar Amurka Auriel Hens, da su ka bayyana cewa; Yadda Isra’ila take amfani da makaman Amurka ya sabawa dokokin wannan kasar da kuma na kasa da kasa, sabanin yadda shugaban kasar Joe Biden yake riyawa.

Har ila yau, da akwai wasu ‘yan Majalisa 40 da su ka yi kira ga shugaban kasar ta Amurka da ya dakatar da sayarwa da Isra’ila makamai.

Ita kuwa tsohuwar shugabar majalisar dokokin kasar ta Amurka Nancy Patricia Pelosi ta shiga cikin masu yin kira ga shugaba Joe Biden da ya dakatar da sayarwa HKI makamai da sauran kayan yaki.



Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments