Sojojin mamayar Isra’ila sun kai harin wuce gona da iri kan yankin Gaza da ya yi sanadiyyar shahadan ‘yan jarida uku, sannan tsuna kai wani harin bam kan asibitin Baptist a Gaza
Rahotonni sun sanar da kashe ‘yan jaridar Falasdinawa uku, yayin da wasu kuma suka jikkata a safiyar Alhamis, a wani sabon laifin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai musu, yayin da sojojin suka sake kai hari kan asibitin Al-Ahli Arab Baptist da ke birnin Gaza.
Majiyoyin kiwon lafiya a asibitin Baptist sun rawaito cewa wani jirgin mara matuki ciki na sojojin mamayar Isra’ila ya kai hari a harabar asibitin, inda ya kashe ‘yan jarida uku tare da raunata dimbin falasdinawa da suka fake a cikin harabar.
‘Yan jaridar biyun da aka kashe an bayyana sunayensu da ‘yan jaridar Falasdinu Today TV Suleiman Hajjaj da Ismail Badah, yayin da wakilin gidan talabijin na Al-Arabiya Islam Badr, da mai daukar hoto Ahmed Qaljah, da dan jarida Imad Dalloul suka samu raunuka daban-daban.