Yau Talata, yan Isra’ila ke kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar wanda aka bayyana cewa zabe ne na yanke hukunci kan makomar firaministan kasar Benjamin Netanyahu mafi dadewa a wannan mukami a tarihin kasar a karkashin jam’iyyar Likud.
Sauran jam’iyyun da ke adawa da Netanyahu sun da jam’iyyar Yashar ta Gadi Eisenkot tsohon babban hafsan sojojin Isra’ila, da hadakar Bennett-Lapid, Yisrael Beit Mana, da kuma Democrats.
Bayanai sun ce bad an takaran da zai iya lashe zaben da gagarimin rinjaye, kasantuwar yadda ‘yan takara ke kud da kud.
Zaben dai na gudana ne a cikin wani yanayi na rarrabuwar kawuna tun bayan harin ranar 7 ga Oktoba, 2023, wanda wasu ‘yan kasar ke zargin gwamnatin Netanyahun da gazawa wajen tabbatar da tsaron ‘yan Isra’ila.
Haka kuma ‘Yan Isra’ila za su kada kuri’unsu a wani yanayi na kisan kare dangi da Isra’ila ta yi a Gaza da kuma shekaru da dama na yake-yake da dama a yankin, wanda ya mayar da kasar saniywar ware a duniya.
Yakin kisan kare dangi da aka yi a Gaza, fadada matsugunan yahudawa da ba bisa ka’ida ba da tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, da kuma ci gaba da fafutukar neman ‘yancin Yahudawa masu tsattsauran ra’ayi, na daga cikin kalubalen da kasar ke fuskanta.
Kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito a ranar Litinin cewa Isra’ila na shirin tura jami’an ‘yan sanda 22,000 a yankunan da aka mamaye domin zaben na yau Talata, domin kauce wa duk wa tashin hankali bayan zaben.