‘Yan Gwagwarmayar Iraki Sun Kai Hare-Hare Kan Birnin Haifa Na Isra’ila

‘Yan gwagwarmayar kasar Iraki sun kai hare-hare kan birnin Haifa da tashar ruwansa da jiragen sama marasa matuka ciki ‘Yan gwagwarmayar Musulunci na kasar Iraki

‘Yan gwagwarmayar kasar Iraki sun kai hare-hare kan birnin Haifa da tashar ruwansa da jiragen sama marasa matuka ciki

‘Yan gwagwarmayar Musulunci na kasar Iraki sun sanar da cewa: Sun kai hare-hare kan birnin Haifa na haramtacciyar kasar Isra’ila sau uku a jere da jiragen saman yaki marasa matuka ciki  a wayewar garin yau Talata, a matsayin mayar da martani kan yadda sojojin yahudawan sahayoniyya suke ci gaba da kai munanan hare-hare kan Zirin Gaza na Falasdinu da kuma yankunan kasar Lebanon.

Sanarwar ‘yan gwagwarmayar Musulunci ya jaddada cewa: An kai hare-haren ne da jiragen sama marasa matuka ciki kan muhimmiyar tashar jiragen ruwa da ke birnin Haifa da sanyin safiyar yau Talata, kuma sun tabbatar da hare-haren sun kai daidai yadda aka tsara su.

Sanarwar ta biyu tana bayyana cewa: Jiragen saman yaki marasa matuka ciki sun yi luguden wuta kan wani muhimmin wuri a birnin na Haifa a karo na biyu, kuma ‘yan gwagwarmaya sun samu tabbacin cewa: Hare-hare suna ci gaba da lalata maboyar makiya cikin sauri.

Sannan sanarwar ta uku ta ce: A yau Talata, sun kai hari a wata muhimmiyar manufa a Haifa a karo na uku, ta hanyar amfani da jirage marasa matuka ciki.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments