‘Yan sandan Uganda sun sanar da cewa mutane 14 ne suka mutu sannan wasu 34 suka jikkata sakamakon wata tsawa da walkiya da ta fada a kan wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke arewacin kasar, wadanda mazauna wurin ke halartar taron ibada.
Mai magana da yawun ‘yan sandan, Ketuma Rusuki ya ce: Har yanzu ba a tantance sunayen wadanda suka mutu ba, kuma hatsarin ya faru ne a wannan Asabar a yankin Lamu mai nisa.
Rosuki ya yi nuni da cewa, ba su samu wani rahoto kan tashin gobara a wurin ba bayan faruwar lamarin.
Mazauna sansanin Palabek, wanda galibi ya hada da ‘yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu, suna halartar taron ibada ne a wani gini da aka yin a majami’ar wucin gadi lokacin da tsawa ta fada a kan ginin da mutane a ciki.
Saud a yawa dai ana samun guguwar isa mai tsanani da ruwan sama gami da tsawa da walkiya a wanann yanki da ke kasar Uganda da ke yankin gabashin nahiyar Afirka.