Wata Cuta Wacce Ba’asanta Ba Ta Bulla Ta Kuma Kashe Mutane Kimani 143 A Kudu Maso Yammacin Kasar Kongo

Mutane akalla 143 suka mutu sanadiyyar bullar wata cuta wacce har yanzun ba’a gane kanta ba, a yankin kudu masu yammacin kasar DM Congo. Shafin

Mutane akalla 143 suka mutu sanadiyyar bullar wata cuta wacce har yanzun ba’a gane kanta ba, a yankin kudu masu yammacin kasar DM Congo.

Shafin yada labaran  Afirka ta yanar gizo, ‘Africa News” ya nakalto hukumomi a kasar na cewa sun fara binci don gano cuta, mai kama da mura, wacce ta bulla a kudancin kasar, take kuma kashe mutane a cikin makonni biyu da suka gabata.

Labarin ya kara da cewa ma’aikatan kiwon lafiya a yankin sun fara tattara bayanan dangane da cutar daga wadanda cutan ta kashe ne, tun ranar 10 ga watan Nuwamban da ya gabata, har zuwa 25 ga watan a garin Panzi na lardin Kwango a kudu maso yammacin kasar.

Sannan kwamishinan lafiya a yankin, Apollinaire Yumba ya fadawa kafafen yada labara kan cewa, alamun cutar sun hada da zazzabi, tari da kuma rashin jini.

Labarin ya kara  da cewa mutane tsakanin 67-143 suka mutu tun bayan bullar cutar  makonni biyu da suka gabata. Ya kara da cewa tawagar likitoci za su isa yankin nan da yan kwanaki don gano irin nau’in cutar da kuma maganinsa.

Banda haka hukumomi a yankin sun yi kira ga kasashen duniya wadanda suke da  kayakin aikin gano irin wadanan cututtukan su kawowa kasar dauki.

Kafin haka dai kasar ta kongo tana fada da cutar kyendan biri (MPOX) wacce ta kama mutane kimani 47,000 kuma ta kashe mutane kimani 1000 daga cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments